Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
    • Privacy Policy
    • Terms Of Service
    • Advertisement
    Monday, July 6
    Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest Vimeo
    ABS Africa TV
    • Breaking News
    • Trending
    • Africa News
    • World News
    • Features
    • Technology
    • Sports
    • Politics
    • More
      • Culture
      • Lifestyle
      • Travel
      • Business
      • Environment
      • Legal
      • Health
      • Cameroon
      • Ambazonia
      • AfroSingles
      • Environ/Climate
      • Editorial
      • The Leak Magazine
    • Donate
    Subscription
    ABS Africa TV
    Home»Lifestyle»Jaruma Halima Abubakar ta koma addinin Kiristanci daga Musulunci
    Lifestyle

    Jaruma Halima Abubakar ta koma addinin Kiristanci daga Musulunci

    Jamia NdamukongBy Jamia NdamukongJuly 6, 2026No Comments4 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
    Post Views: 11
    • Jaruma a babbar masana’antar fina-finai a Najeriya, Halima Abubakar ta sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci
    • Halima Abubakar wadda ta yi suna a masana’antar fina-finai, ta bayyana cewa sauya addinin da ta yana da nasaba da warakar da ta samu
    • Jarumar ta bayyana cewa ta kwashe shekaru tana fama da rashin lafiya wanda ya jefa ta cikin mawuyacin hali da wahala

    Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

    ​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al’amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

    FCT, Abuja – Jarumar fina-finan Nollywood, Halima Abubakar, ta bayyana dalilin da ya sa ta yanke shawarar barin addinin Musulunci domin komawa addinin Kiristanci

    Halima Abubakar tace sauya addinin ta ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin samun waraka ta mu’ujiza daga wata cutar asiri da ta sa ta kwashe kusan shekaru tara a kwance

    Jaruma Halima Abubakar ta masana’antar Nollywood
    Hoto: Nollywoodcitadel Source: Instagram

    Jarumar ta bayyana cewa shekaru da dama tana fama da rashin lafiyar tare da tsallake rijiya da baya a lokuta da dama, rahoton jaridar Tribune ya nuna hakan

    Halima Abubakar ta godewa Ubangiji

    Halima Abubakar ta ce ta gamsu cewa Ubangiji Ya ba ta dama ta biyu ta rayuwa, wanda hakan ya zaburar da ita wajen sadaukar da kanta don bauta ga Yesu Almasihu

    A cewar Halima, farfadowarta ba kawai komawa ga koshin lafiya ba ne, a’a, wani sauyi ne wanda ya gamsar da ita ta bayyana sabon addininta a fili kuma ta fadi abin da ya faru ga sauran mutane, jaridar The Sun ta kawo labarin

    Meyasa ta koma Kiristanci?

    “Ni sabuwar mutum ce yanzu. Na ba da rayuwata ga Almasihu. Ina so na bawa Allah gaskiya domin Ya taimake ni. Na kusan mutuwa. Sun kusan kashe ni. Wannan ba batun fina-finai ba ne; wannan magana ce ta mayar da abin da aka rasa da kuma shaida. Halima Abubakar ta dawo, cikin karfi da kwarin gwiwa.”

    “A yanzu haka, a shirye nake na bawa Ubangiji gaskiya domin Yana so na yi hakan. Ya cece ni, saboda haka ina bukatar in bauta Masa kuma na yi wa mutane wa’azin bishararsa.”

    Ta shirya yin bayani

    Halima ta kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta bayar da shaida a fili da ke bayyana dalla-dalla yadda, a cewarta, Ubangiji Ya taimake ta, ta hanyar cocim Queen Belemzy Ministries (School of Power) don dawo mata da lafiyarta bayan shekaru na wahala

    A farkon wannan shekarar, jarumar ta bayyana cewa mai gidan da take hayar gidanta ta umarce ta da ta tashi daga gidan duk da cewa tana da shirin sabunta hayarta

    Halima Abubakar ta koma addinin Kiristanci
    Jaruma a masana’antar Nollywood, Halima Abubakar
    Hoto: Nollywoodcitadel Source: Instagram

    Ta kuma bayyana cewa har yanzu tana karbar magani, wanda hakan ke nuna irin nauyin bacin rai da na kudi da rashin lafiyar tata mai tsawo ta janyo mata

    Tare da sabon bayyanawar tata, Halima ta ce tana barin shekaru na zafi da rashin tabbas a baya yayin da take shiga abin da ta bayyana a matsayin sabuwar rayuwa ta imani, waraka, da mayar da abin da aka rasa

    Jarumin fim ya rasu

    A wani labarin kuma, kun ji cewa masana’antar fina-finan Nollywood ta yi rashin fitaccen ɗan wasa, marubucin wasan kwaikwayo mai suna Kola Oyewo

    Kafin rasuwarsa, Oyewo ya bayyana matsalolin lafiyarsa a wani bidiyo da ya yi tare da jarumi Kunle Afod a shekarar 2024

    Fitaccen jarumin, wanda ya rasa matarsa a shekarar 2020, ya bayyana yadda likitoci suka sanar da shi cewa yana fama da kumburin mafitsara

    Asali: Legit.ng

    Authors:

    Sharif Lawal (Hausa Editor)Sharif Lawal ma’aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

    Tags:Yan Najeriya FimKannywoodJarumar Fim

    Abubakar addinin Halima Jaruma koma
    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    Jamia Ndamukong
    • Website

    Related Posts

    “He’s still in SA?”: Ndoyisile Sibindi’s Durban July attendance sparks questions

    July 6, 2026

    “Thank you for clarifying”: SA reacts to a clip of Seputla Sebogodi and friends

    July 5, 2026

    HK Music Star – Nimeipenda

    July 5, 2026
    Leave A Reply Cancel Reply

    Search
    Latest Post

    Street photography, Gen Z dances turn Nairobi’s streets into a tourist attraction

    July 6, 2026

    CS Duale demands $1.3 trillion climate fund for Africa at COP29

    July 6, 2026

    China’s Chery takes over former Nissan car factory in South Africa | Business World Philippines – newspaper

    July 6, 2026

    Dis-Chem Pharmacies navigates growth and strategy. Investors weigh South African healthcare trends

    July 6, 2026

    Nigeria condemns killing of two citizens in South Africa, warns of international action

    July 6, 2026

    Subscribe to Updates

    Get the latest creative news from FooBar about art, design and business.

    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • TikTok
    ABS TV and ABS Network News is a leading Pan-African 24/7 broadcasting network delivering nonstop news, talk shows, lifestyle programs, and digital media content worldwide through Satellite, Streaming Platforms, and Roku TV.
     
    Based in the United States, we connect Africa to the world while empowering creators, journalists, and brands through innovative media and broadcasting services.
    Facebook X (Twitter) Pinterest WhatsApp Instagram

    Our Picks

    Street photography, Gen Z dances turn Nairobi’s streets into a tourist attraction

    CS Duale demands $1.3 trillion climate fund for Africa at COP29

    China’s Chery takes over former Nissan car factory in South Africa | Business World Philippines – newspaper

    Most Popular

    Dis-Chem Pharmacies navigates growth and strategy. Investors weigh South African healthcare trends

    Nigeria condemns killing of two citizens in South Africa, warns of international action

    “He’s still in SA?”: Ndoyisile Sibindi’s Durban July attendance sparks questions

    © 2026 Copyright. All Rights Reserved by ABSAFRICATV
    • Privacy Policy
    • Terms of Services

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.

    We use cookies to ensure that we give you the best experience on our website. If you continue to use this site we will assume that you are happy with it.